
Hukumar da ke sa ido kan matsalar abinci ta duniya, Integrated Food Security Phase Classification (IPC), ta bayyana sabon fargaba kan halin matsanancin yunwa da ake ci gaba da fuskanta a Zirin Gaza, inda ta yi gargadin cewa matukar ba a dauki matakin gaggawa ba, akwai yuwuwar asarar rayuka masu tarin yawa.
A cikin wani rahoto da hukumar ta fitar, IPC ta bayyana cewa rashin damar kai kayan agaji da abinci daga kasashen waje zuwa Gaza yana kara dagula halin da al’ummar yankin ke ciki.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da matsa wa Isra’ila lamba ta dakatar da haramcin da ta kakabawa kai kayan taimako ga yankin Falasdinawan.
A cewar rahoton, mutum daya cikin uku a Gaza na kwana ba tare da samun abinci ba, lamarin da ya nuna tsananin matsi da yunwa da al’ummar yankin ke fuskanta.
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya bayyana cewa yanayin ya kai matakin da ya cancanci a dauki matakan jin kai na gaggawa domin kare rayukan fararen hula.
Haka kuma, rahotanni daga asibitoci a yankin sun tabbatar da karuwar mace-macen yara ƙanana ‘yan ƙasa da shekaru biyar, sakamakon rashin abinci mai gina jiki da cututtukan da suka samo asali daga yunwa.