
Sanata Natasha a zauren Majalisar Dinkin Duniya yayi gabatara da koken
INEC ta karbi takardar neman yi wa Sanata Natasha kiranye daga Majalisar Dattijai daga ‘yan mazabar Natasha bisa zarge-zargen dabam-dabam
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta karɓi ƙorafi da ke neman fara yunƙurin yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye a matsayin Sanata.

Sakataren hukumar, Rose Oriaran-Anthony ce, ta karɓi ƙorafin a ofishinn hukumar a yau Litinin.
Ƴan mazaɓar, a karkashin jagorancin Misisi Charity Ijesse ne suka gabatar da wasikar korafin dawo daga rakiyar Sanatar a wakilcinsu a Majalisar Dattawa.
Masu korafin, karkashin ƙungiyar Concerned Kogi Youth and Women, sun yi kira ga INEC da ta gaggauta sahale yunƙurin kiranyen, wanda su ka ce hakan hakan na da kyau wajen karfafa dimokuraɗiyya a Najeriya.
Sun kuma samu sa hannun ‘yan mazabarta 250,000 daga cikin jimillar mutane 480,000 dake dauke da katin zabe a mazabar Kogi ta tsakiya inda Natasah take wakilta, wanda hakan ya cika ka’idar da hukumar INEC take bukata.
Hakan ya zo ne bayan da tun a farko, kotu ta hana INEC karɓar korafi na yunkurin yi wa Natasha kiranye, amma kuma wanne tudu wanne gangare, sai kotun a yau Litinin ta baiwa hukumar zaben damar karbar korafe-korafen.