Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci wani taron gaggawa tare da manyan hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin tattara bayanan sirri domin tattauna batun barazanar Shugaban Amurka, Donald Trump, kan yiwuwar ɗaukar matakin soji a kan Najeriya.
Taron ya gudana ne a ofishin Cibiyar Yaki da Ta’addanci dake Abuja a yammacin Litinin.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa Zagazola Makama, wani mai bibiyar harkar tsaro cewa, manyan hafsoshin tsaron sun tattauna ne kan illolin siyasa da tsaro da ke tattare da kalaman shugaba Trump.
Trump ya zargi gwamnatin Najeriya da gazawa wajen kare Kiristoci daga hare-haren kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Ya kuma yi barazanar cewa Amurka na iya tura dakarunta domin yaƙi da masu tayar da hankali a ƙasar.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta yi watsi da wannan zargi, tana mai cewa babu wata barazana ta musamman da Kiristoci ke fuskanta a ƙasar.
