
Gwamnatin Jihar Kano ta gabatar da rahoton binciken kwamitin da aka kafa don gano musabbabin yanke albashin wasu ma’aikata a watan Fabrairu.
Sakataren Gwamnatin Kano Umar Faruq Ibrahim ne ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai.
“Rahoton ya nuna cewa yanke albashin ka iya kasancewa sakamakon matsalar na’ura mai kwakwalwa ne ko kume kuskuren dan Adam.
“An dakatar da yanke albashin kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf na nazarin rahoton domin daukar matakin da ya dace.” In ji shi.

Kwamitin ya bankado ma’aikatan bogi da ke karbar albashi ba bisa ka’ida ba, kuma an bukaci wadanda ba su bayyana don tantancewa ba su dauki kansu a matsayin korarru.
Za a dauki matakai don tabbatar da ingancin biyan albashi da kare hakkin ma’aikatan da suka cancanta.