
Shahararriyar ‘yar wasan daga dauyi ta Najeriya, Folashade Oluwafemiayo, ta sake rubuta sunanta a tarihin duniya a gasar Zakararun Daga Nauyi Ta Duniya da ake gudanarwa a birnin Cairo, kasar Masar.
Oluwafemiayo ta daga nauyin Kilogiram 168, wanda ya wuce tsohon nasararta ta baya na daga nauyin Kilogiram 167, lamarin da ya tabbatar mata da lashe kyautar zinariya ga Najeriya.
Wannan bajintar ta kara tabbatar da karfinta da kuma daidaituwarta a wannan fanni, inda hakan ke nuna cewa ita ce mafi karfi a rukunin mata a gasar daga nauyi a duniya.
Wannan nasara kari ne a jerin manyan nasarorin da ta samu a wannan wasa, kasancewarta ta hudu a gasar cin kofin duniya, baya ga kyautar zinariya biyu da ta taba lashewa a gasar Paralympics.
Ayyukanta masu ban mamaki suna ci gaba da zama abin koyi ga ‘yan wasa da masoya wasannin daga nauyi, inda take zama abin alfahari da kwarin gwiwa ga sauran Najeriya .