Daga Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) ta ce, ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓen cike gurbi na kansiloli a mazabun Kofar Mazugal da Matan Fada da ke hukumomin Dala da Ghari.
Shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Mulumfashi ne ya bayyana hakan ranar Litinin.
Ya ce zabukan sun biyo bayan rasuwar kansilolin da ke wakiltar mazabun biyu.
Ya ce zaɓen zai gudana ne bisa tanadin sashi na 30 na dokar zaɓe ta shekara ta 2022.
Farfesa Sani Lawan Malumfashi ya kara da cewa zaɓen cike gurbin zai gudana a ranar 13 ga watan Disamba na 2025.
Ya kuma bayar da tabbacin shirin su na gudanar da sahihin zaɓe cikin gaskiya da adalci.
Hukumar ta yi ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Kano da al’ummomin kananan hukumomin Dala da Ghari bisa rashin jagororinsu.
