
Hukumar Shari’a tare da haɗin gwiwar Kungiyar Matasan Musulmai Ta Duniya(WAMY) sun gudanar da shan ruwa ga sabbin musulmai.
An gudanar da taron shan ruwan ne a Kano a ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ali Dan Abba a ranar Litinin
A yayin taron, hukumar ta sanar da ware ranar 15 ga watan kowanne Ramadan da ya kasance ranar da za ta riƙa shan ruwa da wadanda suka musulunta a kowace shekara.
Sheikh Ali Dan Abba ya kuma gode wa Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf da kuma ƙungiyar WAMY bisa goyon bayan da suka bayar wajen gudanar da shirin.
Shi ma wakilin shugaban WAMY, Sanusi, ya nuna farin cikinsa da yadda shan ruwan ya gudana cikin nasara.
A jawabinta a madadin sabbin musulmai, A’isha Suraj ta bayyana jin daɗinsu bisa karramawar da ake yi musu.
A nasa ɓangaren, Kwamishina na Daya a Hukumar Gwani Hadi ya yi kira ga al’umma da su taimaka wajen auren matan da suka karɓi Musulunci.