
Hukumar Hisba anan Kano ta samu nasarar kama mutane 26 a otel din Grace Palace dake kan titin Katsina Road daura da barikin sojoji na Bucavu, wanda take zarginsu da aikata badala.
Dakarun Hisbar da suka kama matasan sun bayyana cewa sun kama mata 14 da kuma maza 12
Mataimakin babban kwamandan Hisba Mujaheeden Aminuddeen ne ya bayanawa wakilinmu Khalil Ibrahim Yaro.Mujahidden Aminuddeeen ya kuma ce dakarun nasu sun samu nasarar kama matasan ne sakamakon bayanann sirri da suka samu.
Hukumar ta hisba tace haryanzu kofarta a bude take duk wanda suke da korafe korafe da ake aikata wani abu da yasabawa sharia za’a iya sanar musu domin daukar matakin gaggawa.