Hukumara Gudanarwa ta Babban Birnin Tarayya Abuja ta bayyana cewa za ta rufe wasu ofisoshin jakadanci 34 saboda rashin biyan harajin filaye tun daga shekarar 2014 da Jimlar kudin da ya kai fiye da Naira Miliyan dubu 3.6
A ranar 26 ga watan Mayu ne Minista Nyesom Wike, ya bayar da umarnin fara kwace kadarori har guda 4,794 da ba su biya harajin filaye ba tsawon shekaru 10 zuwa 43.
To said ai shugaba Tinubu ya shiga tsakani inda ya bayar da wa’adin kwanaki 14 ga wadanda abin ya shafa da su biya duk wani bashi da ake binsu, wa’adin dake karewa a yau Litinin.
Daga cikin ofisoshin jakadancin da abin zai shafa akwai Ghana, Thailand, Côte d’Ivoire, Rasha, Philippines, Netherlands, Turkey, Guinea, Ireland, Uganda, Iraq, Zambia, Tanzania, Jamus, Venezuela, Korea ta Kudu, India, Sudan, Jamhuriyar Nijar, Kenya, Zimbabwe, Ethiopia, da kuma Indonesia.
Sai dai wasu ofisoshin sun musanta ikirarin, Mai magana da yawun Ministan Abuja, Lere Olayinka, ya ce gwamnati za ta binciki duk wani ikirari da ofisoshsin jakadanci suka yi na cewa ba su da bashi, kuma za a dauki matakin da ya dace.
Rahotanni sun nuna cewa wannan hali na ba sani ba sabo kan biyan harajin ya rutsa da wasu daga cikin cibiyoyin gwamnati da suka hada da, Hukumar Haraji ta Tarayya (FIRS), da kuma Hukumar Yaki da Fataucin Mutane (NAPTIP), da Jam’iyyar PDP duk sun biya bashin da ake bin su.
