Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa ta sallami jami’anta fiye da 100 a tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025, a wani yunƙuri na aiwatar da gyare-gyare a cikin hukumar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata a shafinta na yanar gizo, ta ce an fitar da sunaye da hotunan jami’an da abin ya shafa domin ankarar da jama’a.
Hukumar ta ce, jimillar jami’ai 115 ta sallama daga aiki saboda dalilai daban-daban da suka shafi aiwatar da tsare-tsaren sabunta tsarin aiki.
- Kungiyar ISWAP na shirin kai hari a wasu jihohin Kudu – DSS
- DSS ta gurfanar da shugabannin Ansaru da ‘ke da alaƙa da fasa gidan yarin Kuje.
- DSS Ta Sake Kama Mai Garkuwa da Mutane Filin Jirgin Sama
“A wani ɓangare na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a hukumar DSS, an sallami jami’ai 115. Don haka ana gargaɗin jama’a da su guji yin hulɗa da waɗannan mutanen da aka sallama daga aiki,” in ji sanarwar.Hukumar ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na tsaftace hukumar da tabbatar da ingantaccen aiki da gaskiya a tsakanin jami’anta.
