
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta fara rabon muhimman kayayyakin aikin Hajji ga maniyyatan jihar da za su tafi kasa mai tsarki domin sauke farali a bana.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi, ya fitar ga manema labarai a ranar Talata.
A cewar Darakta Janar na hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, an fara rabon kayayyakin ne ga maniyyata daga kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa da kuma Bebeji.
Shugaban ya bayyana cewa kayan da aka raba sun hada da na tufafi da jakunkuna da sauran muhimman kayan amfani da hukumar Saudiyya ta amince da su.
Sannan ya bukaci maniyyata da su yi amfani da kayan da aka rarraba musu yadda ya dace, tare da kaucewa daukar kayayyakin da aka hana shiga da su kasar Saudiyya.
Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba amfani da katin ATM wajen karɓar kuɗin alhazai, yana mai cewa hakan na haifar da matsaloli ga maniyyata.
Ya jaddada cewa hukumar na kokarin ganin maniyyata sun shirya sosai don gudanar da aikin hajji cikin tsari da kwanciyar hankali.