Shugaban Sashen Hausa na BBC tare da wasu manyan Jami’an tashar sun ziyarci gidan Radiyon Premier a Kano.
Shugaban Sashen Hausa Aliyu Tanko da manyan jami’an tashar na bangaren kasuwanci sun kawo ziyarar ne a ranar Talata a inda aka kewaya da su sassa daban-daban na gidan.
Malam Aminu Mohammed Jolly shi da manyan jami’an gidan suka tarbe su a madadin shugaba Malam Abba Dabo.
Jami’an sun kuma gana da manyan ma’aikatan gidan da niyyar karfafa alaka da kuma aiki tare kasancewar gidan na daya daga cikin kafofin yada labarai da suka shahara a cikin jihar Kano da kuma wajenta
Ziyarar ta zo a daidai da kuma ranar da gidan rediyon ke cika shekar uku cif-cif da kafuwa
Ga Yadda ziyarar ta kasance a cikin hotuna