Kungiyar 20 na masu sauraron tashar ne suka halarta inda suka kuma shiga gasar da cin kyaututtuka
A ranar Laraba ne aka gudanar da gasar kacici-kacici na musamman a tsakanin kungiyoyin sa kai kuma masu sauraron tashar a jihar kano.
An shirya gasar ne domin murnar cikar tashar shekara uku da soma gabatar da shirye-shiryenta. Gidan radiyon ta kuma watsa shi kai tsaye a ga masu sauraro ta radio da kuma dandalin sada zumunta na Facebook da kuma shafi tashar na intanet
Yayin da ake gudanar da shi a dandalin wasanni na harbar gidan radiyon da ke kan titin Race Course a unguwar Nassarawa a babban birnin jihar.
Ga yadda taron ya kasance cikin hotuna.