
A ranar juma’a ne ana tsaka da bukukuwan Sallah wuta ta tashi a kasuwar waya ta Farm Center a birnin Kano.
Kafin a Jami’an Kashe Gobara su yi maganinta ta yi barna mai waya da aka kiyasata sun kai na miloyion Naira.
Ga kadan daga irin barnar da gobarar ta yi cikin hotuna:




‘Yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki don rage radadin abin da suka yi hasara da kuma la’akari da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki.
Hukumar Kashe Gobara da Agajin Gaggawa Ta Jihar Kano ta bayar sanarwar cewar fashewar Batirin Sola ne musabbani tashin gobarar.
An kiyasta shugana 300 ne gobara ta shafa a inda suka kone kurmus da kayyakin cikinsu baki daya.