
Hukumar Kwastam ta musanta rade-radin da ake yi cewa za ta dawo da nau’in harajin nan na kashi huɗu cikin ɗari da ake cirewa na shigar da kaya cikin ƙasar, wanda ake kira ”FOB”, wanda aka ɗage aiki da shi a ƴan watannin baya.
Al’amarin da hukumar ta ce, ko da za a ci gaba da aiki da wannan haraji, sai an zauna da dukkan masu ruwa da tsaki, a tattauna da su.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar AbdulLahi Aliyu Maiwada ne ya bayyana haka ga BBC, inda ya ƙara da ba zai yiwu a dawo da karɓar harajin ba ta bayan fage ba tare da an zauna an daddale tare da fahimtar juna ba.