
An gano garin ne sakamakon wani binciken dan jarida da kai ziyara.
Rahotanni sun ce an gano yadda sama da mutane 10,000 ke ganin likita domin duba lafiyarsu amma a karƙashin wata bishiya sakamakon rashin asibiti.
Garin mai suna ƙauyen Baita na yankin karamar hukumar Gezawa ne a jihar Kano.
Wata matar aure, Aliya Alƙasim, wadda ta kawo jaririyarta mai fama da rashin lafiya, fuskarta cike da damuwa, na fatan samun waraka tare da taimakon likitan ƙarƙashin wannan bishiya.
Aliya ta shaida wa jaridae Aminiya cewa, mazauna wannan wuri na fama da rashin asibiti, idan yara ba su da lafiya sai a rasa inda za a kai su.
Sama da shekara goma ke nan da wannan bishiya ta zama cibiyar kula da lafiya a matakin farko a garin Baita, mai yawan al’umma kimanin 8,000 a jihar Kano.
A karkashin bishiyar ake shimfida tabarmi da mutane ke zama domin bin layin ganin likita, kuma haka al’amarin yake a kowanne yanayi na zafin rana, ko sanyi, ko damuna.
Bayan lalacewar asibitin sha-ka-tafi da gwamanati ta gina shekara 30 da suka gabata, yanzun mutanen yankin sun dogara ne da wani shago mai mai ciki biyu ƙarƙashin wannan bishiya domin duba lafiyarsu.
