
Dadga Khalil Ibrahim Yaro
Bokan ya yi tuban muzuru bayan da sauya unguwa daga Kuntau zuwa Rijar Zaki don cigaba da damfarar matan jama’a.
Dakarun Hisbah a jihar kano sun samu nasarar kama wani gawurtacen boka da ya zauna a unguwar Kuntau a Karamar hukumar Dala da kuma Rijiyar Zaki.
Dakta Mujahideen Aminuddeen Mataimakin Babban Kwamandan rundunar ne ya bayyana haka a hirarsa da wakilinmu a ranar Litinin.
Mataimakin Shugaban ya ce, wannan shine karo na biyu da suka kama mutumin da aikata wannan lafifi kansancewar da farko an yi mi shi gargadi ya kuma yi alkawarin daina wa bayan yi mi shi nasiha, amma kuma ya cigaba da aikata laifin.
“Wannan boka ya dade yana yaudara tare da gurbata halayyar yaran mutanne. Da a unguwar Kuntau ya ke a Karamar Hukumar Dala bayan ya yi tuban muzuru sai ya koma RiJiyar Zaki ya ci gaba da tsatsubarsa” in ji Dakta Mujahid.
Sai dai a wannan karon hukumar ta sha alwashin kai shi gaban kuliya sakamako tuhumar da hukumar take yi masa na yaudarar matan jama’a da sunan magani.
Rundunar ta matsa kaimi wajen kau da badala a musamman a ‘yan kwankin nan kasancewar kusantowar watan azumin Ramadana