
Hukumar Hisbah ta jihar Kano na shirin gudanar da auren zaurawa kimani 2,000
Mataimakin Babban Kwamanda Hukumar, Sheikh Mujahid Aminudeen ne ya bayyana hakan hirarsa da manema labarai a ranar Alhamis.
Shieikh Mujahiddeen ya ce kuma ce, za a fara aikin rajista da kuma gwajin lafiya ga duk ma’auratan da ke son shiga shirin nan ba dadewa ba.
“Gwajin lafiyar ya haɗa da na cutar nan mai karya garkuwar jiki. Wato HIV/AIDS da ciwon hanta na Hepatitis, da kuma nau’in jini (genotype)
“Gwajin amfani da miyagun ƙwayoyi wajibi ne, kuma duk wanda ya bijirewa yin sa to bai cancanci shiga shirin ba.” In ji shi.
Sheikh Aminudeen ya bayyana cewa manufar gwajin ita ce tabbatar da lafiyar ma’aurata da kare su daga matsalolin aure da na lafiya a nan gaba.