Rundunar sojin Amurka ta bayyana lalata wasu wurare fiye da 15 da aka ɓoye makamai mallakar mayaƙan ISIS a kudancin Syria.
Rundunar ta ce ta yi wannan aiki ne da haɗin gwiwar ma’aikatan Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Syria a farkon makon nan a Damascus.
Babban kwamandan rundunar, Admiral Brad Cooper ya ce, ya yi amannar cewa mayaƙan ba za su iya kai wasu hare-hare ko ina ba a yanzu.
An dai yi galaba kan mayakan a Syria da Iraqi a shekaru shida da suka gabata.
