
An bayyana matakin da gwamnatin tarayya na samar da sojojin haya don taimaka wajen murkushe ta’addanci a kasar nan a matsayin raguwar dabara.
Tsohon shugaban rundunar haɗin guiwa ta JTF, Dakta Isma’il Tanko Birnin Kudu ne ya bayyana haka a hirarsa da wakiliyarmu a ranar Talata.
“Kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali kan horas da zaratan matasa maimakon dogaro da sojojin ƙetare, baya ga horaswa, gwamnati za ta samar da kayan aikin zamani domin inganta tsaro.” In ji shi
Wannan furuci na masanin na zuwa ne bayan da Ministan Tsaro Badaru Abubakar ya bayyana daukar sojin haya don horar da sojoji 800 a Kaduna.
Gwamnati za ta yi hakan ne don maganin matsalar ‘yan bindiga dake ƙara tsanani, musamman a arewacin Najeriya, inda ake garkuwa da jama’a don karɓar kuɗin fansa da kuma aiwatar da kisa.