
Kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin sufurin kasa ya bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga Ministan Sufuri, Sa’idu Alkali da ya gurfana a gabanta kan yadda jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya yi hatsari wanda ke ɗauke da fasinjoji 618 a kwanakin baya.
Kwamitin ya ɗau matakin ne a ranar Talata, biyo bayan gazawar da ministan ya yi na gurfana a gabanta domin amsa tambayoyi kan lamarin.
Shugaban kwamitin,Blessing Onuh wacce ta nuna rashin jin daɗinta kan rashin zuwan Alkali, ta ce ba za a amince da wannan ɗabi’a ba, ta juya wa ‘yan Nijeriya baya a lokacin da suka fi bukatarsa ba.
Onuh ta ce, Ba zai yi wu ba, su bar ayyukan su, da yawa daga cikin su sun yanke hutun da suke kai, suka taho daga Legas saboda wannan zama amma Ministan ya yi watsi da kiran majalisar.