Shugaban Ƙaramar Hukumar Shanono, Abubakar Barau ya yaba da aikin jam’ian tsaro na daƙile harin ƴan ta’adda a wasu yankunan yankin a ƙarshen makon.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙaramar hukumar Comrade Ammar Shanono ya fitar ga manema labarai a safiyar Litinin.
“Abubakar Barau ya kuma godewa gwamnatin tarayya da kuma ta jiha bisa jagorancin gwamna Abba K. Yusuf bisa yadda suke taimakawa ta kowanne fanni domin ganin an samu zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
“Sannan ya buƙaci al’ummar Faruruwa da su cigaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai don ganin an samu zaman lafiya garin da kuma yankin baki daya,” In ji sanarwar.
Sanarwa na zuwa ne bayan da shugaban ya kai ziyarar gani da ido a garin Faruruwa, a inda ya taka ƙafa da ƙafa inda jami’an tsaron suke a ranar Lahadi, inda ya godewa jami’an tsaron bisa wannan gagarumin aiki.
