
Rahotanni na cewa hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a yankin Gaza sun yi sanadiyyar mutuwar akalla Falasdinawa 95, tare da jikkata wasu 440 A cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
An kai hare-haren ne kusa da cibiyar rabon kayan agaji, inda aka samu raguwar ayyukan agaji sakamakon umarnin dakatar da rabon kayan da wata ƙungiya ke jagoranta – ƙungiyar da ake ta jayayya a kai, wadda ke samun tallafi daga Amurka.
Tun kafin kai hare-haren, sojojin Isra’ila sun yi gargadin cewa jama’ar Gaza su guji zuwa wuraren rabon kayan agaji, inda suka yi ikirarin cewa ƙungiyar nan tana da alaƙa da wasu ‘yan ta’adda.
A wata sanarwa da ƙungiyar bayar da agajin ta fitar a shafinta na X, an tabbatar da dakatar da ayyukan jin kai a yankin, abin da ya kara jefa al’ummar Gaza cikin mawuyacin hali, musamman bayan wata doka da Isra’ila ta sanya ta hana shigo da kayan agaji na tsawon fiye da watanni biyu.
Wannan lamari ya kara tsananta halin yunwa da rashin abinci a Gaza, inda al’umma ke fuskantar kalubale mai girma na samun tallafin jin kai.