Kungiyar shugabannin kananan hukumomin ta kasa ALGON, ta ce har yanzu kananan hukumomin ba su fara ganin kudadensu ba, duk da hukuncin da kotun kolin kasar nan ta yi.
A wata hira da BBC, sakataren kungiyar na kasa, Hamisu Anani, ya ce sun yi korafin cewa kudaden da aka warewa kananan hukumomin a kasafin kudin badi ba za su ishe su biyan mafi karancin albashi ba.
A kasafin kudin dai, an warewa kananan hukumomin kimanin Naira tiriliyan 2.
Idan za a iya tunawa kotun kolin kasar nan ta yanke hukuncin biyan kananan hukumomin kudinsu kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya.
