 
        Hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Kano ta sanar da ranar ƙarshe na biyan kuɗin kujerar hajjin 2026
Shugaban Hukumar, Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana haka a yayin wani taro da ya gudanar da jami’an Hajji na kananan hukumomi da ma’aikatan hukumar a ofishinsa, a cewar Kwamared Sulaiman Dederi, Jami’in hulda da jama’a na hukumar.
“Bisa umarnin Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), da kuma tabbatar da shirin, da tafiyar da aikin Hajji mai kyau a badi, duk masu niyyar zuwa Hajji daga Jihar Kano su kammala biyan kuɗinsu da cike takardu kafin ranar 14 ga Disamba, 2025”. In ji shugaban hukumar.
Hukumar ta jaddada cewa ba za’a karɓi wani biyan kuɗi ko yin rijista bayan wannan rana ba, domin nan take za’a fara shirye-shiryen wuraren zama, sufuri da sauran hidimomin walwala a Ƙasar Saudiyya.
Daraktan ya ce, wannan sauyi ya zama dole domin bai wa masu zuwa Hajji isasshen lokaci su kammala biyan kuɗinsu, tare da bai wa hukumar damar shirye-shiryen tafiya cikin nasara kamar yadda.
Wakilinmu Muhd Nafiu Usman ya rawaito mana cewa Dederi ya shawarci duk masu niyyar zuwa Hajji da su ziyarci ofisoshin hukumar a kananan hukumomi, ko hedikwatar Hukumar, ko ɗaya daga cikin ofisoshin hukumar na sassa.

 
           
           
           
           
         
         
         
         
         
        