
Hukumar dake Yaƙi da Cutuka Masu Yaɗuwa a Ƙasa (NCDC) ta tabbatar da mutuwar mutane 172 sakamakon kamuwa da cutar zazzabin Lassa a faɗin ƙasar nan tun farkon wannan shekarar.
A rahoton da hukumar ta fitar, mutum 924 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a jihohi daban-daban na ƙasar.
Rahoton ya kuma bayyana cewa kaso mafi tsoka na masu ɗauke da cutar sun fito ne daga jihohin Ondo mai kashi 35, da Bauchi mai kashi 22, da Edo mai kashi 17, jihar Taraba mai kashi 13, da kuma Ebonyi kashi 3.
Hukumar ta ƙara da cewa sauran jihohi 16 na ƙasar ne ke da sauran kashi 10 na masu ɗauke da cutar.
NCDC ta bayyana cewa mafi yawan waɗanda suka kamu da cutar su ne matasa masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30, kuma maza ne suka fi kamuwa.