Majalisar Dokokin Kano ta bukaci kungiyoyi masu zaman kansu dake jihar da su gabatar mata da wani daftarin da zai ba ta damar samar da dokar da za ta tsaftace sana’ar Gwan-gwan a jihar.
Shugaban Kwamitin Majalisar Mai Kula Da Kasafin Kuɗi kuma wakilin Karamar Jukumar Ungogo Aminu Sa’adu ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai.
A cewar Ungogo, koken da al’ummar Kano suke yi akan masu sana’ar ne a inda suka dade suna fakewa da ita suna ɓarnatar da kadarorin gwamnatin jiha.
“Akasarin makarantun gwamnati da sauran kadarorin da gwamnati ta samar wanda aka yi su tun tale-tale, matasa masu sana’ar gwangwan sun ɓalle karafan sun sace, idan ba’a ɗauki mataki ba, lamarin zai kai inda ba’a zato.
“Samar da dokar zai taimaka wa masu sana’ar musamman wadanda suke da rijistar gwamnati kakkaɓe ɓata garin cikin su wanda suka zama wata gagarumar matsala a cikin al’umma”. Inji shi
Dan Majalisar ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su sanya ido matuka wajen kare kayan more rayuwar da gwamnati ta samar a yankunan su domin cin moriyar su yadda ya dace.