
Gwamnatin Tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Oktoba, a matsayin ranar hutu domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka.
Ministan Harkokin Cikin Gida Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani ta fitar a ranar Talata.
Tunji-Ojo ya taya ’yan Najeriya murnar zagayowar wannan rana mai tarihi, yana mai jaddada muhimmancin kishin ƙasa, haɗin kai da juriya a matsayin ginshiƙai da suka daɗe suna ɗaukar ƙasar tun daga samun ’yancin kai a shekarar 1960 zuwa yanzu.