
Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fi kowace gwamnati ta soja da Najeriya ta taba yi muni.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna ya fadi hakan ne yayin da yake karɓar bakuncin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakara ƙarshen mako,
El-Rufai ya bayyana gwamnatin Tinubu a matsayin “abin kunya ga akidar dimokuraɗiyya.”
Atiku ya kai wa El Rufa’I ziyarar ne a matsayin jaje bayan harin da aka kai wajen ƙaddamar da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Kaduna, inda ’yan daba suka mamaye wajen suka tarwatsa taron.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda gwamnatin jihar Kaduna da El-Rufai suka dinga zargin juna da hannu a faruwar lamarin. Daga bisani kuma, rundunar ’yan sanda ta gayyaci El-Rufai da wasu shugabannin ADC kan batun.
A lokacin ziyarar, El-Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu na kokarin karkata zuwa mulkin kama-karya, inda ya kwatanta shi da Shugaban Kamaru, Paul Biya, wanda ya rike mulki tun 1982.
El-Rufai ya kuma yaba wa Atiku kan rawar da ya taka a gwagwarmayar dimokuraɗiyyar Najeriya, yana mai cewa jama’a na sa ran ƙwarewarsa da shugabancinsa wajen haɗa ’yan adawa.