
Gwamnatin Tarayya za ta sayar da rukunin gidaje 753, da aka ƙwato daga tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele.
Ministan kula da Gidaje na ƙasar Ahmed Dangiwa ne ya sanar da hakan a Abuja, lokacin da ya ke karɓar takardun mallakar gidajen daga hannun hukumar EFCC.
A cikin sanarwar da daraktan yada labaran ma’aikatar Salisu Haiba ya fitar, ta ce ma’aikatar da hukumar EFCC za su kai ziraya ta musamman rukunin gidajen da ke Abuja, don ganin yanayin da gidajen suke.
“Idan aka kammala duk abubuwan da suka kamata, za a sayar da gidajen ne ga ma’aikata da kuma ɗai-ɗaikun jama’a.
“Za kuma mu tabbatar da cewar an samar da tsari mai inganci, wanda zai fayyace yadda za a gudanar da aikin sayar da gidajen ba tare da ƙunbiya-ƙunbiya ba”. In ji shi.
Shugaban hukumar ta EFCC Olanipekun Olukoyede, ya ce sun miƙa gidajen ne ga ma’aikatar bisa umarnin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Hukumar EFCC ta samu nasarar kwato gidajen ne a hannu Emefiele da a kotu bisa mallakarsu ba bisa ka’ida ba, da kuma sauran tuhume-tuhume.