Hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa, Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), ta sanar da dakatar da shirin ta na fara karɓar harajin kashi 15 cikin 100 kan albarkatun man fetur da ake shigowa da su ƙasar nan daga ƙasashen waje.
Mai magana da yawun hukumar, George Ene-Ita, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis.
A ranar 29 ga watan Oktoba, Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da saka wannan haraji kan man fetur da dizel, wanda zai ƙara farashin man da ake saukewa a defo-defo.
Daya daga cikin manufofin harajin shi ne ƙarfafa matatun mai na cikin gida.
Gwamnatin tarayya ta shirya fara aiki da wannan haraji daga ranar 21 ga watan Nuwamba, kafin hukumar ta NMDPRA ta ɗauki matakin dakatarwa.
