Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirinta na gudanar da addu’a da azumi na kwanaki uku domin magance karancin abinci a kasar nan.
Wannan ya biyo bayan suka da martani mai zafi daga al’ummar kasa kan shirin, wanda tun da farko aka tsara addu’ar domin neman taimakon Ubangiji wajen tabbatar da wadatuwar abinci.
Wata takarda da daraktar gudanarwar ma’aikatar noma ta tarayya, Adedayo Modupe, ta sanya wa hannu ta gayyaci daraktoci da sauran manyan ma’aikata domin halartar taron addu’ar a ma’aikatar a Abuja, a ranakun 16 da 23 da 30 ga Yuni, 2025.
Sai dai wata sabuwar sanarwa daga daraktar, ta bayyana cewa an dakatar da shirin addu’ar har sai wani lokaci na gaba, ba tare da bayyana dalili janyewar ba.
Wannan matakin ya biyo bayan suka da jama’a suka yi a shafukan sada zumunta kan rashin dacewar shirin.
Masu sukar sun bayyana cewa kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali wajen samar da tsare-tsare na gyara dabarun noma da tallafawa manoma da kuma inganta rarraba abinci, maimakon dogaro da addu’a wajen shawo kan matsalar yunwa da hauhawar farashin abinci.
