Gwamnatin tarayya ayyana ranar Laraba 25 da Alhamis 26 ga watan Disamban 2024 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Litinin.
A cewar sanarwar Tunji-Ojo ya miƙa gaisuwarsa ga ƴan Najeriya, sannan ya yi kira gare su yi amfani da lokacin bukuwan domin nuna ƙauna da kira ga zaman lafiya.
Ya ce gwamnati a shirye take ta cigaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro da ci gaban ƙasar, sannan ya taya kiristoci murna, tare da musu fatan alheri.