Sanarwar ayyanawar ta fito ne daga Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Kula Da Harkokin Cikin Gida, Magdalene Ajani da aka yada a kafofin yada labarai a ranar Lahadi a Abuja.
Gwamnati ta ware ranar ce ta Alhamis 12 ga wannan wata na Yuni, a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar dimokradiyya ta bana.
A cewar Ajani, Ministan ma’aikatar Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, inda ya taya ‘yan kasa murnar samun shekaru 26 na mulkin dimokuradiyya ba tare da tsaiko ba.
Ministan ya kuma kara jaddada kudirin gwamnatin Tinubu na tabbatar da dorewar tsarin dimokuradiyya, yana mai cewa shirin shugaban kasa na Renewed Hope Agenda ya warewa tagomashi na musamman ga tsarin mulkin dimokuradiyya dama dorewarsa a kasar nan.
Ya kuma kara tabbatar da bayar da damar dorewar yancin fadin albarkacin baki, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen bunkasa siyasa, ala’ada da tsarin zamantakewar kasar nan.
