Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin bankin abinci na ƙasa mai suna National Foodbank Programme domin ƙarfafa samar da abinci da kuma sauƙaƙa samun abinci mai gina jiki ga yan Najeriya masu rauni.
Shirin, wanda Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ke jagoranta, na da nufin tallafa wa talakawa, musamman mata da yara ta hanyar tsarin rarraba abinci na al’umma.
Ministan Noma da Tsaron Abinci, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa shirin wani muhimmin mataki ne daga tallafin gaggawa zuwa tsari mai dorewa na rarraba abinci a ƙasa baki ɗaya.
Ya ce miliyoyin yan Najeriya na fama da ƙarancin abinci mai gina jiki, musamman yara ƙanana, lamarin da ke nuna buƙatar ɗaukar matakan da suka dace cikin gaggawa.
Kyari ya ƙara da cewa shirin ya dogara ne kan haɗin kai tsakanin al’umma da gwamnati domin tabbatar da gaskiya, inganci da dorewar tsarin rarraba abinci.
Rahotanni sun nuna cewa shirin zai haɗa samarwa, tattarawa da rarraba abinci tare da haɗin kan al’umma domin rage asarar amfanin gona da kuma tabbatar da wadataccen abinci mai gina jiki.
Ana sa ran wannan shiri zai taimaka wajen rage yunwa, ƙarfafa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma a faɗin Najeriya.
