Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce gwamnatin tarayya ta fara ɗaukar matakai na laluɓo wasu hanyoyin samar da lantarki ga jihohin Arewa.
Ya bayanna hakan ne bayan wata ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a wannan Litinin.
Ministan ya ce za su yi hakan ne domin rage raɗaɗin rashin wutar da yankin ke fama da ita sakamakon lalatacewar layukan samar da wutar.
Ya ce za’a fara amfani da wata kwarya-kwaryar tashar bayar da lantarki ta Ikot Ekpene wadda ta taso daga Calabar domin kai lantarki yankin arewa, amma layin ya lalace.