
Gwamnan Jihar Neja Umar Bago
Gwamnan jihar Neja Umaru Bago ya bayar da umarnin dakatar da Hawan Bariki a da sauran bukukuwan Sallah a dukkan masarautun jihar Neja.
Umurnin ya biyo bayan mummunan bala’in ambaliya da ta yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi a garin Mokwa da kewayenta.
Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Abubakar Usman a lokacin da yake mika wannan umarni, ya ce an dauki matakin ne a matsayin girmamawa ga wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma ba da damar zaman makoki da addu’o’i a gare su.
Da yake mika umarnin Gwamnan ga Masarautun, Sakataren ya bayyana cewa, ambaliyar Mokwa na daya daga cikin mafi munin annoba da ta afku a jihar tsawon shekaru da dama da suka gabata, wacce ta yi sanadin salwantar rayuka da rugujewar gidaje da ababen more rayuwa da dama.
