
Hastsarin kwale-kwalen ya rutsa da ‘yan kasuwa ne da suka taso daga ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar Kogi zuwa kasuwar Ilushi a jihar Edo.
A wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar kogi, Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Laraba ta ce gwaman jihar ya jimanta wannan mummunan lamarin.
Gwamna Ahmed Usman Ododo ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma umurci hukumomin da abin ya shafa ciki har da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha da su haɗa kai da ƙananan hukumomin yankin, wajen bayar da tallafi da kuma agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.
Gwamna Ododo ya ƙara da ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ƙara ƙaimi tare da hadin-gwiwa da hukumomin dana gwamnatin tarayya.