Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sayi karin manyan motocin sufuri don ragewa al’umma wahalar zirga-zirga.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin kaddamar da manyan motocin sufuri masu amfani da iskar Gas ga Kungiyar Kwadago NLC wanda shugaba Bola Tinubu ya bayar, a ranar Laraba.
Gwamnan ya kuma ce gwamnati za ta gina wurin gyaran manyan motocin da aka samar.
Sannan ya ce, gwamnatin Kano ta gyara manyan motocin da gwamnatin baya ta yi watsi da su tare da bai wa makarantu domin jigilar dalibai. Sannan wasu daga cikin manyan motocin za su cigaba da jigilar marasa karfi a fadin jihar.
Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya bukaci kungiyar kwadago NLC da ta cigaba da gwagwarmayar tabbatar da walwalar ma’aikata a kasar nan.
Sannan ya yaba wa shugabancin kungiyar karkashin Joe Ajero bisa ziyarar da suka kawo jihar Kano da fadar gwamnati.
Ya kuma yi alkawarin gwamnatin Kano za ta bayar da wuri don gina da aza harsashin katafariyar cibiyar kungiyar a jihar Kano.