
Mataimakin gwamna tare da 'yan kwamitin bayan mika musu takaradar kama aiki a ofishinsa
Gwamnatin jihar Kan ta kuduri aniyar kafa a kwalejin fasaha a Karamar Hukumar Gaya. Ta kuma kaddamar da kwamitin mutum 15 da zai sa ido kan yadda za a aiwatar da hakan.
Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo wanda kuma yake rike da mukamin kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar ne ya kaddamar da kwamitin a ofishinsa a ranar Laraba.
Da yake jawabi a bikin kaddamarwar, Kwamared Gwarzo ya bukaci mambobin kwamitin da su yi aiki tukuru tare da bin ka’idojin da aka shimfida.
Kwamitin yana karkashin Dokta Hadi Bala Yahaya, babban sakatare a ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar, yayin da Shehu Sani Dauda, daraktan gudanarwa da ayyuka na ma’aikatar zai kasance sakatare.
An ba kwamitin mako biyu ya mika rahotonsa.