Gwamnan jihar Kano na shirin inganta ayyukan Hukumar Kula Da Zirga-Zirgan Ababen Hawa a jihar KAROTA ta hanyar sauya masu inifom da ya dace da zamani da kuma sauran ayyuka na kwarewa.
A wata sanarwa da Kakakin Gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce, Sauya Inifom din na daga cikin ayyukan da gwamnatin ta shirya gudanarwa domin inganta ayyukan KAROTA na kula da zirga-zirgan ababen hawa.
Gwamnan ya fadi hakan ne a wani taron bikin mika wasu motoci 29 da gwamnatin ta gyara su a gidan gwamnatin jihar da aka gudanar a ranar Talata
Hakan kuma a cewar sanarwar za ta sa ‘yan Karotan su da iya magance aikata manya laifuka kamar fasa kwauri da kuma fataucin miyagun kwayoyi a jihar, inji sanarwar.
Gwamnan ya kuma yi kira ga jami’an Karota da su rika gudanar da ayyukansu da mutunta jama’a musamman direbobin da kuma ‘yan adaidaita sahu la’a kari da irin rawar da suke takawa na tatattalin arzikin jihar.