Gwamnatin Kano ta bada wa’adin mako biyu a kai mata rahoton duk wata makaranta mai zaman kanta da ta kara kuɗin makaranta ba bisa ka’idaba.
Shugaban hukumar kula da makarantun masu zaman kansu ta Jihar Kano Kwamared Baba Umar ne ya sanar da haka a zantawarsa da manema labarai.
Ya ce gwamnati ta samu korafe-korafe daga iyaye kan yadda ake ƙara kuɗin makaranta ba tare da tuntubar su ko kuma neman izinin gwamnati ba.
Yace ga duk mai korafi akan makarantar ‘ya’yansa ya garzaya zuwa ofishin wucin gadi na hukumar dake gidan Malamai bayan tsohon dogon banki.
Baba Umar ya bayyana cewa an kafa wani kwamitin musamman domin bincikar dukkan makarantun da suka ƙara kuɗi, tare da gano irin karin da ake yi da kuma dalilan da shugabannin makarantun ke bayarwa.
