
Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da shirin horas da matasa 380 a matsayin rukuni na farko na runduna ta musamman da za ta yi yaki da kwacen waya da ayuukan ta’addanci kan tituna da kuma fadan daba a jihar.
Shirin horaswan na daga cikin tsare-tsaren gwamnatin jihar na ƙara tsaro da yaki da laifuffuka, musamman a yankunan birane da suka fi fuskantar matsalolin da suka shafi satar waya da ayyukan bata-gari.
Yayin da yake karɓar matasan da za a horas, Kwamandan Cibiyar Horaswa, Kyaftin Muhammad Bello Mai Gaskiya (mai ritaya), ya bayyana cewa an kafa rundunar ce don mayar da martani kan laifuffukan da ke barazana ga zaman lafiyar al’umma, musamman satar wayoyi da dabanci da ke addabar titunan Kano.
Ya Kuma ce, darussan da za a koyar da su su ƙunshi hanyoyin rigakafin satar waya, tuka mota ta musamman , horo na motsa jiki, da atisaye na tsari, tare da laccoci daga Hukumar NDLEA da kuma shawarwari daga jami’an Hisbah.
Wasu daga cikin matasan da ke halartar horon sun bayyana farin cikinsu da wannan dama da gwamnati ta ba su, inda suka yi alkawarin bada gudunmawa wajen wanzar da zaman lafiya da kuma yaki da miyagun dabi’u a cikin al’umma.
Bayan kammala horon, gwamnati na da niyyar daukar matasan aiki a hukumance, tare da ba su alawus domin ƙarfafa musu kwarin gwiwa.