Gwamnatin jihar Kano za ta gina gidaje 1,800, guda 50 a kowacce Karamar Hukuma 36 na jihar.
Kwamishinan Yada Labarai Da Al’amuran Cikin Gida, Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya sanar da haka ga manema labarai sakamakon zaman Majalisar Zartaswa jihar karo na 33 da gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a gidan gwamnati, a ranar Litinin.
Kwamred Waiya ya ce, za a samar da gidajen ne domin bawa masu karamin karfi damar mallakar muhalli cikin sauki.
Kazalika, kwamishina Waiya yace Majalisar ta amince da kashe Naira miliyan 164 domin sake aikin gyaran babban Asibitin yara na Asiya Bayero da ke cikin birnin Kano.
Majalisar ta kuma amince a kashe sama da Naira miliyan dubu uku domin aiwatar da ayyukan samar da ruwan sha mai tsafta ga al’umma.
Zaman majalisar ya amince da kashe Sama da Naira biliyan 19 domin aiwatar da manyan ayyuka a fannin ilimi da gina tituna da sauran ayyukan raya kasa da bunkasa tattalin arzikin al’umar jihar Kano
