Majalisar Dokokin jihar ce ta yi wannan doka ta kuma hada da masu tofar da yawu ko majina kan hanya yin fitsari a sha tale-tale da karkashin gadoji dake jihar.
Shugaban Masu Rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala ne ya bayyana haka ga wakilinmu a hirarsu kan sabuwar dokar a ranar Litinin.
Shugaban ya kuma ce sun yi haka ne saboda ya zama wajibi gwamnati ta dauki matakan da za su tsaftace Kano domin shigar da jihar sahun biranen duniya a fannin tsafta da cigaba.
“…Wannan doka za ta tilasta hana zubar da shara a magudanan ruwanmu da karkashin rawun-rawun da kuma karkashin gadoji, inda za ka ga mutane sun zo su mayar da wuraren wajen kwanciya.
“Har ma saboda rashin jin kunya mutum zai tube tsaraicinsa ka ga yana bahaya a titi, wannan duk dokar za ta hana wannan.
“Sannan kuma za ka ga mutum yan kan hanya a cikin mota ko a daidaita sahu sai ka ga mutum yayi kaki ya tofar har ya bata wani, ko kuma ya sha lemo ko ruwa ya jefo shi tita, duk dokar zat hana wannan”. Inji shi.
Dan majalisar ya kuma ce, dokar ta tanadi inda za a kawata irin wadannan wurare da furanni da kuma sauran abubuwan ban sha’awa. Kuma ba birnin kano da kewaye ba, har hedkwatar kananan hukumomi na jihar
Lawan Hussaini Dala ya ce, bayan tarar ta Naira dubu 25, akwai Kuma sauran hukunce-hukunce da dokar ta tanada wadanda za’a yi amfani da su wajen ladabtar da duk wanda aka samu da laifukan