
Gwamnatin Jihar Kano ta fara gudanar da bincike na musamman kan matsalolin samar da tsaftataccen ruwan sha da kuma na noman rani a wasu daga cikin Ƙananan Hukumomin Jihar guda goma sha takwas.
Bincike na da nufin gano musabbabin matsalolin da kuma shirin samo mafita mai ɗorewa domin bunƙasa tsare-tsaren ruwa da noman rani wanda zai taimaka wajen haɓɓaka harkar noma da jin daɗin rayuwar al’umma.
Babbar Daraktar Hukumar Bincike da Adana Muhimman Bayanai ta Jihar Kano, Hajiya Nana Asma’u Jibrin, ta tabbatar hakan a yayin ƙaddamar da kwamitin binciken a ranar Alhamis.
Ta kuma ce, gwamnatin Jihar na ɗaukar matakai don tabbatar da cewa duk yankunan Jihar sun sami tsaftataccen ruwa mai inganci.
Sannan ta yi kira ga kwamitin binciken da ya tabbatar sun yi aikinsu yadda ya kamata, tare da ziyartar dukkan wuraren da matsalolin suka fi taɓa.
Ƙananan Hukumomin da wannan bincike ya shafa sun haɗa da Gaya da Rano da Nasarawa da Shanono da Minjibir da Dawakin Kudu da Bebeji da Tsanyawa da Garin Malam da Karaye da Bichi da Gezawa da Ungogo, Kiru da Bagwai da Albasu da Ghari da kuma Tarauni a cikin wata Sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Rabiu Umar Isah ya fitar.
Wannan gagarumin aiki na nuna yadda Gwamnatin Jihar Kano ke jajircewa wajen magance matsalolin da suka shafi rayuwar yau da kullum, da kuma ƙoƙarin bunƙasa harkokin noma domin amfanin al’umma.