
Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka yayin jawabinsa ga masu zanga-zangar lumana kan malamin a bisa zargin yin batanci ga Fiyayyen Halitta Tsira da Amincin Allah Su tabbata A gare shi.
Masu zanga-zangar sun je gidan gwamnatin Kano ne a yammacin ranar Laraba dauke da kwalaye.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarɓe su tare da yi musu jawabi na su kwantar da hankalinsu sannan su shigar da korafinsu ta hanyar da ta dace domin daukar mataki.
“A yi hakuri a je a rubuto mana takarda, mu kuma zamu dauki mataki. A je a kawo wa Sakataren gwamnatin jihar Kano…
“Amma in kun ba shi, ku tabbatar da cewa an buga muku stamp na cewa an karba saboda ita ce shaidar cewa kun kawo kuma an karba. Mu kuma ku jira mu.” In shi.
Ana zargin Malamin ne da sakin baki kan janibin Manza Allah a yayin wani zaman karatu da yayi a wani masallaci a unguwar Kurna kan sahihancin Mauludi.
Kwanakin baya malamin ya yi irin wannan karatu kan wani hadisi na kwarkwarta wanda ya ta da hankalin al’ummar jihar da har sai hukumar shari’a ta zauna da shi da wasu malamai kan batun.