Gwamnatin Kano ta bada gudummawar naira miliyan 36 ga asusun ‘yan Mazan jiya, domin tallafawa iyalan tsoffin sojoji da wadanda suka rasu, a matsayin girmamawa bisa gudunmawa da sadaukarwar da suka yiwa Najeriya.
Da yake mika gudunmawar Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda Shugaban Ma’aikatan fadar gwamnatin Kano, Alhaji Sulaiman Wali ya wakilta, ya ce an bayar da tallafin ne duba da rawar da tsofaffin sojojin suka taka wajen kare martabar Najeriya a tsawon rayuwar su.
Wali yace daga cikin adadin kudin, naira miliyan 20 ta fito ne a madadin gwamnatin Kano , yayin da wata miliyan 5 din ta fito daga gwamna Yusuf da iyalan sa.
Da yake yiwa Premier Radio karin bayani, Wali yace Gwamna Yusuf ya kuma bukaci shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Kano da su bayar da naira dubu 250 kowanne su, a madadin al’ummomin su, wanda hakan ya kai jimillar kudin ya zuwa naira miliyan 11.
Da yake jawabi a wajen taron, daraktan Sashen ayyuka na musamman na fadar gwamnatin kano , Manjo Janar Sani Muhammad mai ritaya, yace taron na daga cikin shirin da asusun yake gabatarwa duk shekara domin tara Kuɗaɗen da ake tallafawa iyalan tsofaffin sojojin.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa jimillar kuɗin da aka tara a yayin taron ya zarce naira miliyan 39, inda gudummawar ta fito daga gwamnatin Kano, manyan jami’an tsaro, da kuma al’ummar jihar.
