Gwamnatin Kano ta shawarci mazauna jihar da su dinga zuwa cibiyoyin kiwon lafiya domin yin gwaje-gwajen duba lafiyarsu akai-akai, musamman domin kare kan su daga kamuwa da cutar sikari, wadda ta ƙara yawaita a tsakanin jama’a a Najeriya.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a wani bangare na bikin masu cutar ta duniya Kano.
Dakta Labaran ya ce cutar siga na ci gaba da zama barazana ga lafiyar jama’a saboda yadda mutane ke gaza zuwa a duba lafiyar su, sai lokacin da cutar ta tsananta, lamarin da ke haifar da matsaloli wajen magance cutar.
Kwamishinan ya bayyana cewa ma’aikatar lafiyar jihar ta ƙaddamar da shirye-shirye da dama, ciki har da samar da kayayyakin gwaji a asibitoci, da horas da ma’aikatan jinya, da kuma gudanar da wayar da kai a unguwanni domin ƙara fahimtar da jama’a yadda za su kare kansu daga cututtuka masu tsanani da saurin kamuwa.
Dr Labaran ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma, malamai da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su tallafawa gwamnati wajen wayar musu da kai domin yin gwaji da wuri, domin rage mace-mace da inganta rayuwar jama’a.
