Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce tun daga ranar da ya fara shirin fita daga jam’iyyar NNPP, gwamnatin sa ta fara samun cikakkiyar fahimta da hadin kai daga dukkan hukumomin gwamnatin tarayya, musamman a fannin tsaro, lafiya da tattalin arziki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayar da tallafin baburan hawa 600 ga masu tallata manufar gwamnatin sa a kafofin sada zumunta jiya Asabar
Gwamnan yace duk matakan da ya dauka a gwamnatin sa yana yi ne domin ci gaban al’umma da bunkasa Kano, kasancewar jihar Kano da al’ummar cikin ta sune a gaba da komai a tsarin tafiyar da mulkin sa.
Gwamna Abba yace duk abinda ke faruwa a Kano yanzu, yana da alaka da tasirin addu’ar da malamai da mutanen kirki suka yiwa Kano musamman lokacin da gwamnati ta tara malamai suka yiwa jihar tare da neman zabi Allah akan dukkan abinda zai zamo mafita ga Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Abba Yusuf na jaddada kudirin gwamnatin sa na ci gaba da tallafawa mata da matasa a jihar ta yadda zasu zamo masu dogaro da kan su Da tsame su daga munanan dabi’u wanda hakan zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin Kano
